Engr. Sani Bala Tsanyawa ya gabatar da Kudirin da zai sanya kayan abinchi su sauko a Nigeria

Date:

Daga Yakubu Abubakar Sayyeed

 

Dan majalisar wakilai da yake wakiltar kananan hukumomin Kunchi da tsanyawa Hon. Engr. Sani Bala tsanyawa ya gabatar da wani kudiri kan matsalolin da suka haddasa tsadar kayan abinchi musamman shinkafa a kasar nan.

KADAURA24 ta rawaito Dan majalisa Engr. Sani bala ya gabatar da kudirin ne a zauren majalisar wakilai ta kasa, Inda ya bukaci majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da fitar da abinchi daga kasar nan, wanda yace hakan ne musabbabin karancin abinchi da ake samu a kasuwannin wanda kuma hakan ne kan assasa tsadar kayan abinchi a Nigeria.
Da yake gabatar da kudirin Engr. Sani Bala ya baiyana fitar da kayan abinchi musamman danginsu shinkafa wake masara waken suya gero da dai sauransu, da cewa yana kawowa yunkurin gwamnatin tarayya na wadata kasar nan da abinchi tsaiko.
” Gwamnatin tarayya ta kashe kudade masu tarin yawa wajen shirye-shiryen da ta bijiro daso don bunkasa aikin gona a Nigeria, amma yan Nigeria basa ganin kokarin hakan, saboda yadda a koda yaushe ana fitar da kayan abinchi daga kasar nan zuwa kasashen waje, wanda hakan ne ummul aba’isin tsadar kayan abinchi da ake fuskanta a Nigeria “.inji Sani Bala Tsanyawa
Sani Bala Tsanyawa wanda dan yake majalisar tsahon shekaru 7 ya ce idan akai la’akari da matsalolin tsaro da suka hana manoma zuwa gonakinsu don yin aikin noma a wasu jihaohin kasar nan, da kuma matsalar da annubar cutar korona ta haifar, akwai bukatar gwamnatin tarayya ta yi duba aka batun hana fitar da abinchi daga kasar nan zuwa kasashen ketare, wanda in akai hakan zai saukakawa al’ummar Nigeria musamman masu karamin karfi.
Duk da matsala ta karancin abinchi da ake fuskanta a duniya baki daya, amma kullum a Nigeria sai tirela sama 40 zuwa 50 makare da kayan abinchi sun fita da daga Nigeria zuwa makwaftan kasashe”. Inji Engr. Sani Bala
Babu shakka idan gwamnatin tarayya ta yi aiki da wannan kudiri da dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin kunci da tsanyawa ya gabatar al’umma zasu Sami saukin kayan abinchi wanda shi ne abun da yafi ciwa talakawa tuwo a kwarya.
Kamata yayi sauran yan majalisu su marawa wannan kudiri na Sani bala naya domin idan gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da shi to fa alumna kasar nan musamman talakawa zasu sami saukin rayuwa, kuma suma yan majalisun su yi koyi da Engr. Sani balan wajen gabatar da makamancin irin wannan kudiri wanda zai taba rayuwar duk wani dan Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...