Hadimin Ganduje SSA Gwarmai ya sake rabawa matasa kudi, Mashina da Jakai don inganta Rayuwarsu

Date:

Daga Sayyeed Abubakar

 

Mataimaki na musamman ga Gwamna jihar kano a kan harkokin matasa Alhaji Murtala Gwarmai ya rabawa matasa guda shida babura domin saukaka musu a sha’anin sufuri a wani yunkuri na basu damar sharbar romon damakaradiyya.

Da yake zantawa da manema labarai Alhaji Murtala Gwarmai yace ya rabawa matasa babura da jakunan ne domin cika umarnin gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje na tallafawa mata da matasa don inganta rayuwarsu kamar yadda yake yi a matakin jihar.

Gwarmai yace ya zama wajibi ya bada tallafin saboda irin gudunmawar da suka baiwa gwamnatin kano musamman a zaben shekara ta 2019 da ya gabata, da kuma kokarin da suke yi na ganin sun dogara da kawunansu.

A yau mun bada babura guda shida ga matasa sannan daya daga cikinsu yace shi jakai yake bukata domin inganta harkokinsa na Neman abinchi wanda yake gudanarwa don ya rufawa Kansa asiri”. Inji Gwarmai.

Bayan ya rabon baburan Hadimin na Ganduje ya baiwa wasu matasa 4 tallafin naira dubu Dari biyu da hamsin kowannensu tare kuma da mikawa wata mata takardar shidar daukar aiki a ma’aikatar lafiya ta jihar kano.

ina so Ku sani na baku waɗanan babura da kudin ne saboda ku ma Ku sharbi romon damakaradiyya, kuma Mai gidanmu Hon. Murtala Sule Garo ya taka rawa sosai wajen tabbatuwar wannan al’amari don haka idan kuka gidewa Gwamna Ganduje to Ku godewa Hon. Murtala Sule Garo sannan kuma Nima sai ku rabani cikin godiyar”.
Inji SSA Gwarmai

Mai kudi meku da Muhd sani sabalanga na daga cikin wadanda suka amfana da tallafin na wannan lokaci sun godewa Hon Murtala Sule Garo da Hon. Murtala Gwarmai bisa abun alkhairin da S SA din yayi musu, tare kuma da bada tabbacin yin amfani da tallafin ta hanyar data dace.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...