Gwamnatin Kano ta bayyana sunayen unguwannin da aka sami gurbatacciyar Iska

Date:

 

 

Wani rahoto na mako-mako kan yanayin lafiyar iska da gwamnatin Kano ke saki ya nuna cewa akwai gurɓatar iska a wasu unguwanni a cikin ƙwaryar Kano, inda hakan zai ƙara ta’azzara yaɗuwar cuttutuka a cikin al’umma.

Rahoton, wanda Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta fitar bayan gwajin lafiyar iska da ta yi tsakanin 26 zuwa 30 ga watan Mayun da mu ka yi bankwana da shi, ya nuna cewa unguwanni kamar su Gaida, Ja’en, Sabon Titi da Sharada Kasuwa, basu da lafiyayyar iska, inda sakamakon ya nuna akwai gurɓatar iska a waɗannan unguwanni.

 

IMG 20250415 WA0003
Talla

 

Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir M Hashim ne ya wallafa rahoton a shafin sa na Facebook.

Rahoton ya nuna cewa gwamnatin Kano na shirin kai ɗauki a wadannan unguwanni sakamakon gurɓacewar iska, inda ta nuna damuwa kan karin gurɓacewar yanayi da ake samu a jihar.

InShot 20250309 102403344

Ya kuma nuna cewa kula da muhalli hakki ne na gaba daya al’umma ba wai gwamnati kaɗai ba.

Daily Nigerian

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...

Rundunar Sojin Amuruka ta kammala tsara yadda za ta kawo wa Nigeria hari

  Rundunar sojin Amurka da ke Afirka, AFRICOM, ta gabatar...

Kalaman Trump: Gwamnatin Nigeria ta Fara tattaunawa da Gwamnatin Amuruka

Gwamnatin Najeriya ta ce a gwamnantance tana tattaunawa da...

Ba zan bar Siyasa ba har lokacin da zan bar Duniya – Mal Shekarau

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce...