SAMINU IBRAHIM MAGASHI
Sayyada Rahmatullah sheikh Ibrahim Inyas ta jagoranci karantun dala’ilu tare kuma da yiwa masa addu’a domin samun dauwamammen zaman lafiya a Nigeria.
Kadaura24 ta rawaito cewa Sayydarar ta bayyana cewa babban makasudin da yasa suka kira maulidin na bana dana yiwa Kasa addu’a shi ne saboda da irin yanayin da Kasar nan suka ta fada na tabarbarewa tsaro da tashe tashen hankulan al’umma Nigeria.
An dai gudanar taron addu’o’in da saukar dala’ilu ne a masallacin juma’a na Sheikh Ibrahim Inyass dake unguwar Gadon kaya a birnin kanon dabo.
” Matsalolin tsaron da kasar nan take fuskanta akwai bukatar al’umma a kungiyance ko a daidaiku a rika yin addu’ar Allah ya kawowa Nigeria saukin matsalolin tsaro da suka addabi al’umma”.Inji Sayyada Rahmatullah
Shi ma a jawabinsa khalifan tijjaniya na kasa Muhd Sanusi II Wanda yasamu wakilcin Alhaji Mujittafa Falaki ya yiwa daukacin al’umma fatan alkhairi tare da Jan hankalin matasa wajan ganin sunbtashi haikan wajen neman nakansu kasancewar ita ce hanya daya tilo da zata kawo cikakken tsaro a kasar nan.
Ya yabawa wadanda suka shirya taron tare kuma da fatan mutane zasu gyara tsakaninsu da Allah ko a sami saukin matsalolin da suka addabi al’umma.
taron dai ya sami halartar dumbin al’umma na ciki da wajan kasarnan ciki kuwa harda Yaya” da jikokin Shehu Ibrahim Inyass da kuma halifofin tijjaniyya da mukaddamai da muridai da dai sauran manya baki.