Daga Umar Sani K/Naisa
Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara Barr. Mahdi Aliyu Muhd Gusau ya mayar da martani ga Gwamnan zamfara Bello Matawalle, kan ikirarin da yayi na sauka daga kan kujerar Gwamnan jihar.
Barrister Mahdi Aliyu Mohammed Gusau ya ce a shirye yake ya bada takardar barin aikin a matsayinsa na mataimakin gwamnan jahar Zamfara muddin Gwamna Matawalle zai rubuta tashi takardar ta barin mukammin sa na Gwamna kamar yadda yayi ikararri ya yin wata hira da yayi da manema labarai a gidan Gwamnanitin jihar.
A wancan lokacin Gwamnan yayi rantsuwa da Allah cewa ba don sanin da yayi cewa Mataimakin Mahdi Ali Gusau ne zai hau kujerar Gwamna ba bayan shi Matawallen ya sauka, da tuni ya sauka daga kujerar ta Gwamnan.
Da yake mayar da martani ga Gwamnan, Mataimakin Gwamnan yayi Allah waddai da wannan magana wadda ya kira ta tamkar soki burutsu . Ya zargi Matawalle da laifin wasa da hankalin mutannen jihar zamfara.
Cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na Jihar Abba Bello ya Sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24 yace mataimakin Gwamnan ya kara jaddada cewa a shirye yake ya rubuta takardar barin aikin a duk ranar da shi Gwamnan zai rubuta tashi.
Ya kara da cewa wannan kudurri da matamaikin Gwamnan yayi na barin aiki tare da shi da gwamna Matawalle yana daga cikin sadaurkawar da za su yi don ganin an ceto jahar Zamfara daga mummunan halin da ta samu kanta. Ya kuma kara da ba Gwamna Matawalle shawara daya mayar da hankali wajen shirrin yadda zai tafiyar da rayuwar shi bayan ya sauka daga mulki wanda ga dukkan alamu ya kusa.