An Kaddamar da Littafin Tarihin Garin Zawaciki

Date:

Daga Maryam Muhd Zawaciki
An kaddamar da littafin tarihin  garin zawaciki dake karamar hukumar kumbotso a jihar kano wanda Abubakar Yahuza Yakubu Zawaciki ya rubuta.
Da yake bayyana makasudin rubuta littafin Abubakar yahuza yakubu  yace ya wallafa littafin ne saboda yadda garin yake da dadadden tarihi amma kuma babu tarihinta a rubuce.
Abubakar Yahuza yace akwai yara masu tasowa da suke bukatar sanin tarihin garin duba da yadda garin yake kara habbaka tare da samun cigaba a kowanne lokaci.
Marubucin littafin yace ya fuskanci kalubale mai yawa yayin da yake kokarin rubuta littafin, Inda yace ya sami shekaru uku yana rubuta littafin, amma dai yace babbar nasarar da ya samu ita ce kammala littafin.
Yayin da yake nasa jawabin mai garin zawaciki mallam Abdulkhadir mu’azam zawaciki ya nuna matukar farin cikin sa dangane da samar da littafin tarihin garin na zawaciki.
Mai garin yace wannan abin Alfahari ne ka san,cewa garin yana da kyakyawan tarihi kuma a kasamu matashi dan gwagwarmaya ya shiga ya fita har ya samar da tarihin garin zawaciki domin Jama’ar garin.
Mai garin yayi Kira ga matasa da suyi koyi da wannan matashin mai shekara 34 wajen ganin suma suna bawa al’umma gudumawar da tadace.
Shima a nasa jawabin Farfesa Muhammad Bello Shitu  ya nuna farin cikin sa ga Abubakar matashi Dan gwagwarmaya da yayi tunanin bijiro da tarihin kuma bar ya wallafa tarihin  garinnasa.
Farfesa Shitu ya kara da cewa suna da kugiyoyi da suke bawa matasa kwarin gwaiwa wanda Abubakar yahuza yana daya daga cikin matasan da suka tallafawa wajen ganin ya rubuta litafin tarihin garin zawaciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gidauniyar Pyramid of Heart sun kai tallafin na’urar Oxygen Concentrated Asibitin Murtala dake Kano

Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhd dake Kano ya yabawa...

Da dumi-dumi: ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta dakatar da...

Ba mu da wata matsala da Ofishin mataimakin shugaban Kasa – NAHCON

Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta karyata wani rahoto...

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi hukumar NBC ta fadada aikinta kan kafafen yada labarai na intanet

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Hukumar...