Daga Asiya Takalmawa
Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi a wasu bangarori na cewa ya kamata ya ci gaba da zama jagora a maimakon ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2023.
Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labaran fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ta Villa Abuja ranar Litinin din nan.
A cewar jigon na jam’iyyar APC, shi dan Najeriya ne kuma yana da ‘yancin tsayawa takara da kansa, ba wai kawai ya tsaya matsayin jagora ba.
“A ko’ina a duniya Ban taɓa ganin dokar da ta ce wai jagora ba zai tsaya takara ba sai dai ya tsaya a matsayin jagora, ba a haka don haka zan cigaba da neman Shugaban kasa kamar yadda na fadawa shugaba buhari ”. Inji Tinubu
Jigon na jam’iyyar APC ya ce ya je fadar shugaban kasa ne domin sanar da shugaban kasa a hukumance bukatarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Da aka tambaye shi ko shugaban kasar ya aminta da bukatar tasa, Tinubu ya ce shugaban kasar bai nemi ya ajiye bukatar tasa ba ta tsayawa takara.