Wasu fusatattun matasa sun kashe wasu mutane uku da ake zargin ‘yan Bindiga ne, ciki har da mace guda, bayan wani hari da bai yi nasara ba a kan al’ummar Fulani a karamar hukumar Goronyo da ke jihar Sakkwato a ranar Laraba.
Matasan sun kuma kona ofishin kungiyar ’yan banga inda aka ajiye’ yan fashin na dan lokaci.
‘Yan fashin sun zo Rugar ne, da ke wajen Goronyo, da tsakar dare don satar shanu amma sun fuskanci turjiya daga makiyayan wadanda suka kuma kame uku daga cikin maharan.
“Mutanen da ke wurin sun shirya sosai Harsasai ba sa ratsa su. Sun dakile harin, sun kame uku daga cikin ‘yan fashin sannan suka mika su ga‘ yan banga da safe, ”wani mazaunin ya ce.
“Lokacin da labarin kamun ya isa ga samarinmu, sai suka tattara kansu suka mamaye ofishin’ yan banga da ke garin Goronyo inda aka ajiye ’yan fashin na dan lokaci.