Daga Rabi’u Usman
Rundunar Vigilantee ta Jihar Kano ta ce ta Samu Nasarar Dakume Wani Matashi Mai Suna Yunusa da ake Zargin Barawon Awakin Jama’a ne.
Rundunar tace Wannan ba Shi ne farau ba da aka taba Kama Wannan Matashi da Zargin Satar Dabbobin Jama’a ba, Wanda yanzu Haka Dubun Sa ta Cika Bayan da aka Kama Shi da Zargin Satar Awakai guda 3 da Kimar Kudin Su takai Dubu 100.
Babban Kwamandan Rundunar Muhammad Kabir Alhaji ne ya Bayyana hakan yayin da yake Ganawa da Manema Labarai a Wannan rana.
A Nasa Bangaren Matashi Yunusa da ake Zargin Barawon Awakin Jama’a ne ya Bayyana Cewar, ya Sato su a Cikin Daji ne Sannan ya Kawo Su Kasuwar Gomo dake Cikin Karamar Hukumar Sumaila a Nan Kano Amma tsautsayi ne.
A Karshe dai Kwamandan yayi Kira ga Al’umma dasu Kasance Masu Taimakawa Jami’an Rundunar Vigilantee da Bayanan Sirri da Zarar Sunga Motsin Abin da Basu Amince da Shi ba Domin Kawo Musu Dauki na Gaggawa.