Allah ya yiwa Dr. Ahmad Bamba na BUK Rasuwa

Date:

Allah Ya yi wa babban malamin addinin nan na Kano Sheikh Ahmad Bamba Kala Haddasana ya rasu a yau Juma’a.

Wata jikarsa ta tabbatar wa da BBC Hausa labarin rasuwar.

Fitaccen malamin ya yi fice ne a wajen karatuttukan Hadisi, inda a da can yake karantarwar a Masallacin BUK amma daga baya ya bude nasa wajen mai suna Darul Hadis.

Malamin ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya, kuma ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.

Iyalan sun sanar da cewa za a yi jana’izar malamin a Masallacin Darul Hadis da ke unguwar Tudun Yola a birnin Kano bayan Sallar Juma’a.

Za mu ci gaba da kawo muku karin bayani kan labarin.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarki Aminu Ado Bayero ya baiwa Alan Waka Sabuwar Sarauta a Masarautar Kano

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Mai martaba Sarkin Kano na 15...

Soke Hawan Sallah: Dole Gwamnatin tarayya ta biya mu diyya – Gwamnatin Kano

Daga Isa Ahmad Getso   Gwamnatin jihar Kano ta bukaci gwamnatin...

NiMet ta bayyana jihohin da za a sami tsawa da ruwan sama na kwanaki 3 a Nigeria

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya ta...

Hajjin bana: Gobarar ta tashi a otel din wasu Alhazan Nigeria a Makka

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Hukumar kula da Alhazai ta Najeriya...