Dr. Ahmad BUK: Kano ta yi Rashin Rumbun Ilimi, Kuma Mai Koyar da Zaman Lafiya – Ganduje

Date:

Daga Sadiya Muhd Sabo.

 

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana rasuwar Dr Ahmad Muhammad Ibrahim, fitaccen Malamin cibiyar Darul Hadith da ke Kano, a matsayin babban rashi, kasancewarsa cikin jiga-jigai masu samar da zaman lafiya da kuma tarin ilimin Hadisi.

 

Mutuwar a cewar gwamnan ta girgiza  jihar sosai. Ya kara da cewa, malamin ya kasance hazikin malami, mai zurfin hazaka da asali, a karantarwarsa na fadin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

 

Ya kasance mai karfafa zaman tare da kokarin tabbatar da cikin Lafiya, wanda tsarin koyarwarsa ya kasance ta hanyar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin dukkanin bangarori da ma sauran su. Wannan babban rashi ne da ke tattare da bakin ciki da ba za a iya maye gurbinsa,” in ji gwamnan.

 

Cikin Sanarwar da Babban Sakataren yada labaran Gwamnan Malam Abba Anwar ya aikowa Kadaura24 yace Ganduje ya bukaci malaman addinin Musulunci da su yi kokari tare da yin koyi da kyawawan halaye na marigayi Sheikh Dr. Ahmad BUK. Yana mai jaddada cewa, “Ya kafa ginshikin yadda ake yin Da’awa kuma ya bi abin da yake wa’azi akai .

 

 “A madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano, ina mika ta’aziyyarmu ga iyalan Sheikh Dr Ahmad Muhammad Ibrahim, Rashin Malamin ba wai na iyalansa ba ne kawai, Kano ko Nijeriya baki na duk al’ummar duniya ne baki daya “.

 

Ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta masa dukkan kurakurensa, ya kuma saka masa da alherinsa da Jannatul Fiddaus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...