2023: Bayan Rikicin APC a Gombe, Jam’iyyar ta Sulhunta Danjuma Goje da Gwamna Yahaya Inuwa

Date:

Daga Abdulrasheed B Imam

 

Kwamitin Rikon Jam’iyar APC na Wucin-gadi, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya sulhunta tsakanin Gwamna Muhammad Yahaya Inuwa na Jihar Gombe da kuma abokin burmin sa na siyasa, tsohon gwamnan jihar, Sanata Ɗanjuma Goje.

Jami’in Yaɗa Labarai na Shugaban Kwamitin Rikon jam’iyyar, Mamman Mohammed ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Larabar data gabata a Abuja.

Sanarwar ta ce Buni, da Shugaban Kwamitin Sulhu na APC, Sanata Abdullahi Adamu da tsohon Gwamnan Jihar Borno Kashim Shattima, mamba a kwamitin, su ne su ka jagoranci sulhun.

Sanarwar ta ce wannan shi ne karon farko da manyan ƴan siyasar na Gombe su ka haɗu tun bayan da rigimar siyasa ta ɓarke tsakanin su a shekarar bara.

Mai Mala Buni, Matsayin sa na Shugaban Kwamitin Rikon jam’iyyar APC ta kasa ya baiyana jin daɗin sa game da sulhun da a ka yi.

Ya kuma yi alwashin sulhunta duk masu ruwa da tsaki a APC domin ƙarfafa jam’iyar yayin da a ke tunkarar kakar zaɓe ta 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano za ta sake gina Masallacin da aka kona a Gezawa

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna...

Hukumar shari’a ta Kano ta ladaftar da wasu ma’aikatan kotu

Daga Usman Hamza   Hukumar Kula da Harkokin shari'a ta Jihar...

2027: Malam Shekarau ya bayyana matsayar kungiyarsu kan hadakar yan hamayya a Nigeria

Ƙungiyar siyasa ta Northern Democrats, ƙarƙashin jagorancin Malam Ibrahim...

Da Ɗumi-Ɗumi: Dangote ya sake rage farashin man fetur

Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da ƙarin...