Daliban nan 27 da aka sace daga Kwalejin Koyon Gandun Daji ta Tarayya, Afaka, jihar Kaduna, an sake su.
Daya daga cikin mutanen da suka karbi daliban ya tabbatar wa Daily Trust labarin.
Ya ce kwamitin tattaunawa na Sheikh Ahmed Gumi ne ya taimaka wajen sakin tare da goyon baya daga tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Daliban na daga cikin mutane 37 da aka sace kusan watanni biyu da suka gabata.
Bayan biyan kudin fansa daga iyaye da shugabannin makarantar, ‘yan fashin sun saki 10 kawai daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su.
Da farko wadanda suka sace su sun nemi gwamnatin jihar Kaduna ta ba su kudin fansa har Naira miliyan 500 amma Gwamna Nasir El-Rufai ya yi watsi da batun tattaunawar, yana mai cewa ‘yan bindiga sun cancanci kashewa.