Zaftare albashi zai sa ma’aikata cikin kunci – Kungiyar Kwadago

Date:

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta gargadi gwamnatin tarayya da ta dakatar da yunkurin da take yi na rage albashin ma’aikata, tana mai cewa irin wannan mataki zai sa ma’aikata su shiga cikin wani hali na ha’u’la’i.

A ranar Talata ne minister kudi ta Najeriya Zainab Ahmed Shamsuna ta bayyana cewa gwamnati na nazari akan yadda za ta zaftare yawan kuɗaɗen da take kashewa ta hanyar rage albashin ma’aikata.

Rahotanni sun kuma ce ministar ta umarci hukumar albashin ma’aikata ta yi nazari akan albashi da yawan ma’aikatun gwamnati da ke kasar.

Manyan kungiyoyin kwadago hudu da ke yajin aiki a Najeriya
May Day: Kalubalen da ma’aikatan gwamnati suke fuskanta a Najeriya
Sai dai shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Ayuba Wabba ya yi kira ga gwamnati a kan ka da ta zaftare albashin mafi kankanta na naira dubu talatin na ma’aikata, yana mai cewa albashin masu karbar albashi mai tsoka ne kawai ya kamata a rage musamman masu rike da mukaman siyasa.

“Abu ne da ba za a taɓa tsammani ba cewa gwamnati za ta yi niyya ta rage albashin ma’aikatan Najeriya a wannan lokacin”.

”Tambayar anan ita ce shin wani albashi ne gwamnati za ta zaftare? Ko shakka babu ba albashi mafi kankanta na naira dubu talatin ba ne wanda halin yanzu ba ya iya sayan buhun shinkafa.

Shugaban kungiyar kwadagon, yayin da yake bayyana matakin a matsayin “rashin tausayi” da “rashin tunani”, ya ce ma’aikatan Najeriyar na bukatar a gaggauta janyewar matakin tare da neman afuwa daga Ministan Kudin kasar.

157 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...