Tauraruwar fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta ce daga yanzu ba za ta ci gaba da fitowa a shirin nan mai dogon zango mai suna ‘Labarina’ ba.
Kadaura24 ta rawaito a sakon da ta wallafa a shafinta na Intagram ranar Asabar da daddare, tauraruwar ta ce ta ji dadin rawar da ta taka a cikin shirin, sai dai ta ce ba za ta iya ci gaba da shi ba saboda wasu dalilai na kashin kanta.
A Sanarwar da ta Fitar Nafisa tace harkokin Kasuwancinta da Makaranta ne Suka hana ta cigaba da fitowa a Shirin,Inda tace Suna da kyakykyawan fahimta da Kamfanin Saira movies Kuma ba Wata Matsala Suka samu ba.
Amma wasu majiyoyi sun tabbatar wa BBC Hausa cewa ta dauki matakin ne saboda rashin jituwar da aka samu tsakaninta da mai shirya shirin kuma shugaban kamfanin Saira Movies, Malam Aminu Saira.
Nafisa ita ce babbar tauraruwa a shirin na Labarina mai farin jini a tsakanin ‘yan kallo inda take taka rawa a matsayin Sumayya.
Taga Tanada Kudi dole tadingayin wulakanci Yadda takeso