Tsohuwar matar fitaccen tauraron Kannywood, Ahmad S. Nuhu, ta bayyana mawuyacin halin da ta fada a cikin bayan rasuwarsa.
Hafsat Shehu ta bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa a yayin da tauraron yake cika shekara 15 da rasuwa.
Tauraron ya rasu ne ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2007 sakamakon hatsarin mota a garin na jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Ta ce ta fada cikin matukar bakin ciki yadda “idan na ga wasu mutane suna dariya nakan tambayi mahaifiyata cewa .yaushe zan yi dariya’? Sai mama tace ki yi hakuri kema wata rana zaki yi.
Tace duk Lokacin da ta ji wani ya cewa Wata yana son ta sai hankali ta ya tashi Saboda itace kalma ta kace da S Nuhu ya fadamin kafin ya tafi maiduguri wacce kuma ita ce tafiya da bai sake dawowa ba.
” Ahmad mutumin kirki ne Mai mutunta mace da kokarin Ganin ya faranta Mata ta hanyar sauke duk wani nauyi da Allah ya dora Masa ,A Gaskiya nayi rashi masoyi Kuma a lokacin da nake da buƙatar sa.”
Hasfat Shehu bayan ta fashe da koka tace Alhamulillah Allah ne ya bani Ahmad Kuma ya karbi kayansa,Amma dai Ina so ku Sani wallahi ko Wakar sa aka sa ana daga min hankali,Amma dai Ina Yi Masa addu’a a Koda yaushe don nema Masa rahamar Ubangiji.