Gwamnatin tarayya ta ba da tabbacin na ganin an kammala aikin titin jirgin kasa na Kano zuwa Kaduna kuma a shirye take ta kaddamar da shi a watan Disamba 2022.
Rotimi Amaechi, Ministan Sufuri ne ya bayyana haka a lokacin da yake duba yadda aikin ke gudana a Kano.
A cewarsa, za a kammala aikin ne kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar mulki.
Mista Amaechi ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, gwamnatin tarayya ta zuba sama da dala miliyan 400 domin gudanar da aikin.