Shekara 2022 Shekara ce ta sulhu da zaman lafiya – Ganduje

Date:

Daga Aisha Mai Agogo
 Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce ya kamata sabuwar shekara ta 2022 ta kawo sabon zaman lafiya da sulhu a tsakanin masu ruwa da tsaki a jam’iyyun siyasa a jihar nan da ma kasa baki daya.
 Ya ce ya kamata a ce watanni masu zuwa su zama na dimokuradiyyar cikin gida inda za a  samu ci gaba a jam’iyyun siyasar Jihar nan, yace yi hakan zai samar da wakilai masu nagarta a matakai daban-daban wadanda suke da kwarewa wanda su ci gaba da gina kano kan tsare-tsare da manufofin da shugabannin da suka shude suka assasa.
Kadaura24 ta rawaito a sakon sabuwar shekara ga al’ummar jihar wanda kwamishinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya fitar, gwamnan ya ce daga dukkan alamu abubuwan da suka faru a Kano na iya kawo wani sabon salo a tarihin siyasar jihar.
 Ya ce al’ummar Kano dake da kishin cigaban Kano Sun nuna bukatar ganin Manyan ‘yan siyasar Kano sun yi sulhu da juna, domin ganin an samar da zaman lafiya da ci gaba mai inganci a fagen siyasa da al’amuran cigaban al’umma.
 Sanarwar ta nuna matukar damuwa kan yadda ake ta fama da tabarbarewar tsaro a fadin kasar baya ga fatara da ake fama da ita sakamakon tabarbarewar tattalin arziki a kasar.
 Sai dai ya bayyana fatansa na cewa duk da kalubalen da ake fuskanta gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na ci gaba da kokarin ganin an aiwatar da manufofinta da shirye-shiryen yadda za a ragewa al’umma radadin talauci.
 Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin sa, wadda kasafin kudin 2022 ya Mai da hankali wajen kammala ayyuka, da kuduri aniyar kyautata wa al’umma ta hanyar kawo sauyi a yankunan karkara da kuma shirye-shiryen karfafa tattalin arzikin Jihar Kano.
 Yayin da yake taya al’ummar kasar murnar shigows sabuwar shekara, Ganduje ya kuma yi kira da a hada kai da yi wa Najeriya addu’a musamman malaman addini su rika wa’azi akan zaman lafiya, hakuri da juna duk da kalubalen da ake fuskanta.

17 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...