Yan Sanda Sun Kashe Yan Bindiga 38 a Jihar Katsina

Date:

An kashe akalla ‘yan bindiga 38 yayin da ‘yan sanda biyar suka mutu a samame daban-daban da aka kai cikin jihar Katsina.

Rundunar ‘yan sanda jihar Katsina ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana karkashin shugaban ‘yan sandan jihar Sanusi Buba.

Babu shakka wannan shekarar da ta kare an fuskanci kalubale mai yawa a Katsina musamman na tsaro, sai dai rundunar ‘yan sandan jihar ta samu nasarori masu yawa a yakin da take da ‘yan bindiga da masu satar mutane da ‘yan fashi da sauran manyan laifuka da ake aikatawa.

Duk da haka 2021 cikinta an samu raguwar wadannan laifuka idan aka kwatanta da 2020″.

Cikin rikicin an samu nasarar kashe ‘yan bindiga 38 an kuma kashe mana jami’ai 5.”

Rundunar ta ce an kama wasu da ake zargi da muggan ayyuka 999 da suke da alaka da manyan laifuka 608.

A gefe daya kuma an kama wasu mutum 874 na daban da aka gurfanar gaban shari’a a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...