Mutumina da Yace da Shariff Sani Janbulo akai Isra’i ya Karyata Kansa a Yayin da aka Titsiye Shi

Date:

Daga Umar Usman Sani Mainagge
Ma’aikatar kula da harkokin addinai ta yiwa wani bawan Allah Mai Suna Lawan Ibrahim titsiye karkashin jagoranci Kwamishinan Ma’aikatar Dr Tahar adamu Baba Impossible.
Tun a kwanakin baya ne dai Wani mutum mai suna Lawan Ibrahim mazaunin unguwar mundadu dake karamar hukumar kumbotso ya furta wasu kalamai masu tsauri wadanda za su iya tada tarzoma a jihar kano Saboda muninsu a addinin Musulci.
Lawan Ibrahim dai ya furta kalaman ne a wajen wani Maulidi da aka Gudanar a unguwar Ja’en Inda da yace wai “an halicci Sharif Sani Janbulo kafin a halicci Annabi Adam sannan kuma Sharif sanin tare suka yi isra’i da mi’iraji da manzon Allah kuma duk wanda baya son Sharif sani dan wuta ne” inji shi 
Saboda haka ne ma’aikatar kula da harkokin addinai dake gidan murtala karkashin jagorancin kwamashinan ma’aikatar Dr. Tahar Adamu Baba Impossible ta gayyaci Lawan Ibrahim da wanda ya hada maulidin da kuma wanda aka furta kalaman akansa Wato Shariff Sani Janbulo domin Jin yadda lamarin yake don gudun barin lamarin sakaka Kuma a Cigaba da fadin da.
Yayin taron titsiyen Wanda aka gudanar a dakin taro na ma’aikatar wannan mutumi Mai Suna Lawan Ibrahim ya yi mi’ara koma baya tare Kuma da janye kalamansa harma ya karyata da kansa da kansa bayan  ya ji matsa ta tambayoyi da neman hujja akan abun daya furta.
Abun da na fada na yi shi ne bisa jahilci da Rashin Ilimi Amma insha Allah bazan sake furta irin kalaman ga Wani mahalugi ba.” a cewar sa
A ganawarsa da Wakilinn Kadaura24 Wanda ya Shirya taron Maulidin ya tabbatar da Cewa a wajen Maulidinsa aka furta Wadancan kalamai ,amma yace kafin furta kalaman bashi da masaniyar za’a furtasu.
Shi ma a nasa bangaren wanda ake dambarwar akansa Sharif sani janbulo ya ce shi ma bai goyi bayan kaalaman da akai akansa ba Kuma ba’a son ransa akai hakan ba.
Daga karshe kwamashinan ma’aikatar harkokin addinai Dr. Tahar Adamu Baba Impossible yace sun Shirya titsiyen ne domin yiwa lamarin burki don gudun kada a sake Samun Wani ya furta irin kalaman ga Shi Shariff Sani Janbulo Koma Wani daban.
Ya Kuma ce Gwamnatin Jihar Kano bazata lamunci irin Wadancan yasassun kalaman ba , Saboda sun sabawa addinin Musulci da Kuma abun da aka Sani na Ilimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NAHCON ta sanar da ranar da za a fara jigilar Maniyatan Nigeria zuwa kasar Saudiyya

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Hukumar kula da aikin hajji ta...

Hisbah ta rushe wajen da aka ce sawun Ma’aiki ya fito a jihar Kano

    Hukumar Hisbah ta kai samame tare da rushe wani...

ƴan siyasa ne su ka kashe Arewacin Nigeria — Inji Gwamna Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa ‘yan...

Shugaban Karamar hukumar Bagwai ya kaddamar da aikn gada ta sama da Naira Miliyan 160

Daga Shu'aibu Sani Bagwai   Karamar hukumar Bagwai a jihar Kano...