Jami’ar European-American ta fitar da sanarwa da ta ke barranta kan ta da digirin girmamawa da aka baiwa shahararren mawaki, Dauda Kahutu Rarara ba, inda ta ce ba da izinin ta kuma ba ta yarjewa kowa ya bada digiri ga mawaƙin ba.
A wani taro da aka shirya a otal din Nicon Luxury a Abuja a jiya Asabar, wanda gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya halarta tare da wasu manyan baki, an baiwa Rarara wannan digiri na girmamawa ta hannun wasu mutane da suka nuna kansu a matsayin wakilan jami’ar.
Amma a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin ta na yanar gizo, muhukuntan jami’ar sun nisanta kan su da Rarara da kuma jami’an da suka nuna kansu a matsayin wakilan jami’ar.
“Jami’ar ba ta ba da izinin gudanar da wani bikin kammala karatu a wannan wuri a yau ba, kuma wannan taron an shirya shi ne ta hanyar damfara ba tare da sanin jami’ar ba ko amincewarta.

” Wadanda suka shirya wannan taron sun yaudari wasu mutane cewa su ne wakilan Jami’ar European-American, amma wannan ba gaskiya ba ne, kuma ba su da wani hurumin yin hakan ko karbar kudi a madadin jami’ar,” in ji sanarwar.