Daga Maryam Adamu Mustapha
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Fati Muhammad ta dawo Kannywood bayan shafe shekaru goma sha hudu da daina sana’ar.
Dawowar Fati ta kasance tare da fatan alheri daga masoyanta da masoyan fina-finan Hausa.
Ta dawo ne a matsayin mai shirya fina-finai kamar yadda wata ‘yar gajeriyar sanarwa ta bayyana a shafin Facebook na ‘Kannywoodcelebrities.
A Ranar talatar nan dai sabbin hotunan Jarumar sun karade shafukan Sada Zumunta musamman Facebook da instegram Wanda hakan ke nuni da Cewa al’umma Suna farin Ciki da dawowarta harkar Fina-finan Hausa.
KADAI ta rawaito an dai nuna hoton Fati Muhd a zaune kan Wata kujera yayin da ake daukar wani sabon fim Wanda zata taka rawa a Cikin sa, Kuma za a iya Cewa Shirin shi ne na Farko bayan dawowarta harkar Fina-finan Hausa.
Fati ‘yar asalin jihar Adamawa ta fara harkar fim tun tana karama, Fina-finan ta da suka yi fice a Cikin su sun hada da Sangaya, Zarge, Marainiya, Mujadala, Kudiri, Tutar So, Garwashi, Tawakkali, Gasa, Abadan Da’iman, Zo mu Zauna, Tangarda, Hujja, Al’ajabi, Halacci, Samodara, Zumunci, Murmushin Alkawari, Gimbiya, Bakandamiya, Taskar Rayuwa, Babban Gari da dai Sauransu.