Daga Abdulrasheed B Imam
Wata Kungiyar mai suna alkalami ya zarta takobi da hadin gwiwar gaskiya dokin karfe karkashin jagorancin Malam Naziru Musa Shehu Marmara ta kaddamar da wani Littafi Mai takenbSo ake yiwa Annabi S A W wanda ya kunshi bayani Kan soyayyar Ma’aikin Allah (S A W).
Malam Naziru Musa Marmara shi ya rubuta Littafin Kuma a zantarsa da wakilin Kadaura24 yace ya rubuta Littafin ne da nufin kara cusawa al’umma son Manzon Allah A W tare Kuma da banbance irin son da za a yiwa Ma’aikin .
“Littafin ya yi bayani sosai Kan irin nau’in soyayya da Kuma Kauna ,tare da bayyana irin Wacce za a yiwa Ma’aikin Allah tsira da aminchin Allah su tabbata a gare shi, don Haka muke ganin Littafin Zai amfanar da al’ummar Musulmi sosai’ Inji Mal Naziru Marmara
Malam Naziru Marmara ya Kara da Cewa an kaddamar da littafin ne domin tinasar da al’umma so za a yiwa Annabi ko kauna za’a nunawa Masa da Kuma yadda za a yi.
Yayin taron an Karrama Wasu Mutane Waɗanda Shugaban kungiyar malam naziru ya ce sun karrama mutanan ne saboda jajircewar su wajan hidimtawa al’umma .
Waɗanda aka karrama sun hada da Sheikh Askiya Sheikh Nasiru Kabara Sai Mai Wuddadu da Usman Muhammad Tahir mai dubun Isa da dai sauran su.
קמגרה למכירה במודיעין פעמים רבות אנחנו יודעים שאנחנו צריכים לעשות משהו, אבל “רק הפעם” פשוט נמנעים מלעשות את זה, פשוט כי זה דורש יותר מדי מאמץ. אותו הדבר ������� ������� ��� �������