An Kaddamar da littafi Mai taken “So ake yiwa Annabi ko Kauna” 

Date:

Daga Abdulrasheed B Imam
Wata Kungiyar mai suna alkalami ya zarta takobi da hadin gwiwar  gaskiya dokin karfe karkashin jagorancin Malam Naziru Musa Shehu Marmara ta kaddamar da wani Littafi Mai takenbSo ake yiwa Annabi S A W wanda ya kunshi bayani Kan soyayyar Ma’aikin Allah (S A W).
Malam Naziru Musa Marmara shi ya rubuta Littafin Kuma a zantarsa da wakilin Kadaura24 yace ya rubuta Littafin ne da nufin kara cusawa al’umma son Manzon Allah A W tare Kuma da banbance irin son da za a yiwa Ma’aikin .
“Littafin ya yi bayani sosai Kan irin nau’in soyayya da Kuma Kauna ,tare da bayyana irin Wacce za a yiwa Ma’aikin Allah tsira da aminchin Allah su tabbata a gare shi, don Haka muke ganin Littafin Zai amfanar da al’ummar Musulmi sosai’ Inji Mal Naziru Marmara 
 
Malam Naziru Marmara ya Kara da Cewa an kaddamar da littafin ne domin tinasar da al’umma so za a yiwa Annabi ko kauna za’a nunawa Masa da Kuma yadda za a yi.
Yayin taron an Karrama Wasu Mutane Waɗanda Shugaban kungiyar malam naziru ya ce sun karrama mutanan ne saboda jajircewar su wajan hidimtawa al’umma .
Waɗanda aka karrama sun hada da Sheikh Askiya Sheikh Nasiru Kabara Sai Mai Wuddadu da Usman Muhammad Tahir mai dubun Isa da dai sauran su.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...