Rahotanni daga Katsina na cewa gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda na cikin koshin lafiya bayan da tawagar motocinsa ta yi hatsari a kan hanyar Daura zuwa Katsina.
Wani jami’in gwamnatin Katsina da ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar wa da DCL Hausa faruwar hatsarin.

Ya ce wata mota ce ta gogi ayarin motocin gwamnan, lamarin da ya haddasa hatsarin.
Sai dai ya ce gwamnan jihar na cikin koshin lafiya, amma akwai wani jami’in gwamnan da ake tunanin ya ji raunin da ba mai tsanani ba.