Iyalan mafarautan da aka kashe a Edo sun zargi gwamnatin kano da yin watsi da su

Date:

Iyalan mafarauta 16 ’yan Jihar Kano da aka yi wa kisan gilla a garin Uromi da ke Jihar Edo sun yi zargin cewa gwamnati ta yi watsi da su.

Wasu daga cikin waɗanda suka tsallake rijiya da baya a harin da kuma iyalan waɗanda aka kashe, sun bayyana cewa alƙawarin kuɗin magani da tallafi da kuma diyya fa gwamnatocin jihohin Edo da Kano suka yi musu bai wuce fatar baki ba.

Ayarin farautan sun baro garin Fatakwal na Nijar Ribas ne, a hanyarsu ta komawa gida domin bikin Ƙaramar Sallah, amma wasu ’yan banga a Uromi suka tare su, suka yi musu kisan gilla.

InShot 20250309 102512486
Talla

Akasarin mafarautan sun fito ne daga yankin Toronkawa da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure ta Jihar Kano, tare da abokansu daga ƙananan hukumomin Garko da Kibiya da Rano.

Yan kaɗan daga cikinsu ne suka sha da ƙyar a harin na Uromi na ranar 28 ga watan Maris, wanda ya sha tofin Allah-tsine daga ɓangarori daban-daban.

’Yan sanda sun bayyana cewa sun kama mutum 14 bisa zargin hannunsu a harin, a yayin da gwamnatocin jihohin Kano da kuma inda abin ya faru, suka yi alƙawarin ɗaukat matakan da suka dace na tallafi ga waɗanda abin ya shafa da iyalansu da kuma tabbatar da cewa an hukunta masu laifin.

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

A watan Afrilu Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya sanar da kafa kwamitin bincike na haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya kan lamarin.

Gwamna Okpebholo ya sanar da haka ne bayan mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci jami’an gwamnatin Kano suka yi takakkiya zuwa Edo bayan kisan da aka yi wa Kanawan.

Daga bisani Okpebholo ya kai ziyarar ta’aziyya Kano, inda ya yi alƙawarin biyan diyya ga iyalan mamatan da kuma majinyatan da harin ya shafa.

A nasa jawabin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya jagoranci Okpebholo zuwa garin Toronkawa, ya jaddada cewa gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an biya cikakken diyya ga iyalan. Ya kuma yi musu alƙawarin tallafi na kuɗaɗe da kayan abinci.

 

Gwamnatocin Kano da Edo sun yi gum
Daily trust ta tuntuɓi Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, wanda kuma mamba ne a kwamitin binciken, kan dalilin rashin cika alƙawuran da gwamnatin jihar ta yi wa mutanen da abin ya shafa, amma ya ƙi cewa komai.

Haka shi ma Kwamishinan Jihar Edo, Paul Ohonbamu da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan jihar, Free Itua, ba su amsa kiranmu ba ko rubutattun tambayoyin da aka tura musu ba.

Wakilinmu ya tuntuɓi shugaban al’ummar Hausawa a Jihar Edo, Alhaji Badamasi Saleh, amma ya bayyana cewa ba shi da masaniya game da ko gwamnatin jihar ta biya diyyar da ta yi wa mutanen alƙawari.

Ba a cika mana alƙawari ba

A garin Toronkawa kuma, iyalai da ragowar mafarautan da harin ya shafa sun ce ba a cika alƙawarin ba.

Ɗaya daga cikin mafarautan da ya tsallake rijiya da baya, Ibrahim Isah, ya tabbatar da hakan, inda ya ƙara da cewa, “Yanzu da ƙyar nake iya kula da iyalina. Yarana ’yan ƙanana ne ballantana su tallafa min.

“An yi mana alƙawarin za a kula da mu a asibiti, amma daga aljihuna na kashe kuɗin jinya N40,000, duk da haka ban samu kulawar da ta dace ba.”

Ya ce duk da alƙawarin tallafin abinci da sauransu da Gwamnatin Kano ta yi musu, amma ba su gani a ƙasa. “Sun ce sun kawo mana kuɗi da abinci, amma dai ba mu komai ba.

“Mun je sakatariyar ƙaramar hukuma, aka ce ciyaman ya tafi Saudiyya, amma mataimakinsa ya ce suna aiki a kan lamarin,” a cewar Malaman Ibrahim ɗan shekara 45.

Malama Zahura Haruna, matan ɗaya daga cikin mafarautan da aka kashe, ta ce, “Rayuwa ta yi mana ƙunci, yanzu na zama nauyi ga surukaina, da ma shi ne mai ƙarfin gidan. Yanzu da maƙwabta muka dogara don samun abinci.”

Amma Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kibiya, Nasiru Adam Abdulaziz, ya jaddada aniyar ƙaramar hukumar ta nema wa waɗanda abin ya shafa adalci.

Ya ce, “Waɗannan iyalan sun cancanta a yi musu bayani kuma ina da ƙwarin gwiwa cewa gwamnati za ta yi abin da ya dace.”

Daily Trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Malam...

Gwamnatin Kano ta bada hutun sabuwar shekarar Musulunci

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana gobe Alhamis, 26 ga...