Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Date:

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu Barhama Suleiman da Jamilu Ahmad a garin Makurdi na jihar Benue.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, an kai harin ne da misalin karfe 11:00 na dare a ranar Litininda wasu ’yan bindiga suka kaddamar.

InShot 20250309 102512486
Talla

Gwamnan ya bayyana matukar alhininsa kan wannan mummunan lamari, inda ya bayyana lamarin a matsayin rashin hankali.

Ya yi Allah-wadai da kashe-kashen da aka yi da kakkausar murya tare da ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar na bakin kokarinta wajen ganin an hukunta wadanda suka aikata laifin.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa shi da kan sa zai jagoranci wata tawaga mai karfi da suka hada da iyalan marigayin, zuwa sallar jana’izar da aka shirya gudanarwa a babban masallacin kasa dake Abuja a yau 24/06/2025.

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Da yake jajantawa iyalan wadanda suka rasu, Gwamnan ya jajanta wa fitaccen malamin addinin musulunci Sheikh Ibrahim Khalil, wanda shi ne uban mutanen biyu da aka kashe.

Gwamna Yusuf, ya bayyana rashin a matsayin abin takaici ga iyalai da abin ya shafa, kuma illa ga jihar Kano da ma kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...