Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Date:

Daga Zainab Nasir Ahmad

Mai Girma Gwamnan Kano,
Abba Kabir Yusuf
Abba K Yusuf

Cikin alhini da rawar jiki na ke rubuta wannan wasiƙa, a matsayina na ƴar jahar Kano. Ƴar Kano wacce ke cikin firgici da damuwa da ganin yadda a kullum yanayin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a jiharmu. Jihar da a da ta ke amintacciya da ƙima, ta rikiɗe ta zama kamar filin dagar da jini ke kwarara. Jinin bayin Allah, ƴan jihar Kano!

Kwanaki biyu da suka wuce, akan hanya ta ta komawa gida daga wajen aiki na biyo ta ɗaya daga cikin irin wannan unguwanni da ke fama da irin wannan tashin hankali a motata na tarar da “go slow” ashe ba “Go Slow” ba ne, ɓata gari ne su ke ta’adar su kamar yadda su ka saba yi. Ba da ban ina da sauran kwana ba a duniya na tabbatar da tuni sai dai a ce “Hajiya Zainab marigayiya”

Galibin yaran da na gani riƙe da muggan makamai, yara ne ƙanana. Kallo ɗaya za kai musu ka fahimci a tunzire su ke. Fuskokinsu a murtuke ba annuri. Ba wai faɗan dabar ya tsaya tsakaninsu ba ne kaɗai, kan mai uwa da wabi su ke. Akan ido na ga suna fasa gilasan motoci, suna ƙwace wayoyin jama’a ta ƙarfi da yaji.

InShot 20250309 102512486
Talla

A wannan hali idan na ce ban firgita ba gaskiya na yi ƙarya, don hannuwana karkarwa kawai su ke yi, jikina kuwa yana ta ɓari. A haka dai na yi ta addu’a, ina neman mafita a wajen Allah daga wannan bala’i da ya ritsa da ni. Daga ƙarshe dai Allah ya taimake ni kafin su farmun na juya motar, na samu kafa na tsira.

Bayan na tsallake rijiya da baya, na zauna na yi zugum a mota, jikina a sanyaye, can na ji hawaye ya jiƙa fuskata.
Hawaye ne na takaici da jin zafin cewa yau Kano, garinmu yara su ke wannan ɓarnar ido na ganin ido.

Mai girma Gwamna, wannan ba zancen siyasa ba ne. Wannan shi ne halin da mu ke ciki a Kano. Kano yanzu ta zama kwata da jini ke gudana!

Iyaye da dama a kullum suna rasa ƴaƴansu, saboda wannan rikici.
A yanzu ta kai iyaye suna tsoron su bar ƴaƴansu mata fita daga gida. Ƴan kasuwa a yanzu bisa dole su ke rufe shagunansu, ba wai saboda rashin ciniki ba, sai don tashin hankalin da ake ciki na faɗan daba da ƙwace.

Fadan Daba a Birnin Kano, Laifin Waye? – Barr. Hadiza Nasir

Wannan ɓata gari a kullum ƙara samun ƙwarin gwiwa su ke. Ta kai yanzu taruwa su ke su shiga saƙo da lungun suna ta da tarzoma. In mutum ya lura sosai zai fahimci wannan matasa kamar suna tura saƙo ga sauke fushinsu ne ga ƴan gari bisa yaudara da da ƴan siyasa ke yi wajen amfani da su lokacin zaɓe, sannan su watsar da su bayan biyan buƙatarsu.

Duk yadda mu ka kai da kawar da kai cewa aikin yaran nan ba babba ne, yaudarar kanmu mu ke, maganar gaskiya a yanzu a Kano rayuwar kowa tana cikin hatsari.

Mai girma Gwamna, lallai ne mu ƙara zage dantse, wajen kawo ƙarshen wannan annoba, don a duk daƙiƙa ɗaya da mu ƙara wajen sako-sako kan lamarin nan kamar ƙarin daƙiƙa ne na rayuwar al’umma tana cikin haɗari.

Mai girma Gwamna ga shawara ta a taƙaice da na ke ganin za su kawo ƙarshen wannan annoba, kamar haka;

1: A zartar da dokar ta ɓaci wato “State of Emergency” akan daba da ƙwacen waya da duk wani nau’i na tarzoma da matasan ne ke yi. Domin yanzu kamar muna cikin halin yaƙi ne, don haka wajibi ne mu mayar da cikakken hankalinmu da ganin mun yi duk ƙoƙarin mu don mu kai ga nasara. A yanzu dai kawo ƙarshen wannan annoba shi ya fi kamata gwamnati ta mai da hankali a kai, fiye da komai.

2: Mu ƙarfafi ƴan bijilante da sauran mutanen gari, saboda sun fi kowa sanin abubuwan da su ke faruwa da wanda ke yin wannan ta’adar. Taimaka musu da kayan aiki don kare unguwanninsu bisa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro abu ne muhimmi.

IMG 20250415 WA0003
Talla

3: Tabbatar da an hukunta wanda ke ɗaukar nauyin yaran nan duk girmansu zai taimaka ƙwarai. Don asalin wannan tarzoma tana da alaƙa da wasu jiga-jigan manyan mutane da ke ɗaukar nauyin yaran nan, wajen basu muƙamai da kayan shaye-shaye. Bayyana sunayen wannan manyan da gurfanar da su ga hukuma, ya zama wajibi.

4: Lallai ne mu ƙirƙiri cibiyoyi da za su dunga kawo “Programs” don kuɓutar da matasan nan daga shaye-shaye, yakasance sun zama masu jan hankalin matasan nan, kamar: Koyar da sana’o’i, wajen motsa jiki ko wasanni, shawarwari, da “rehaiblitation” ga ƴan shaye-shaye. Yakasance duk ƙaramar hukuma an samar irin wannan cibiyar.

5: Gabatar da wani tsari na lumana da ƙoƙarin janyo hankalin wannan ɓata gari don su tuba su bar wannan miyagun ayyuka ta hanyar amfani da gidajen, makarantu, masallatai da sabbin hanyoyin sadarwa na zamani wato “Social Media”

6: Gwamnati ta haɗa kai da ƙungiyoyin sa kai wato “Civil Societies Organizations” Da yawan wannan ƙungiyoyin sa kai sun yi nisa wajen wannan aiki, a yanzu ma a shirye mu ke wajen ilimintar, da duk abin da ake buƙata. Babban abin mu ke buƙata daga wajen gwamnati shi ne goyon baya ɗari bisa ɗari!

Mai Girma Gwamna, ina mai roƙonka gwiwata a ƙasa a matsayina na ƴar Jihar Kano da ta tsallake rijiya da baya daga hannun wannan matasa, da a taimaka a duba shawarwari na, a ceto Kano daga halin da ta ke ciki. A duba mutunci da ƙima da daraja ta jiha

Fassara: Mukhtar Mudi Sipikin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...