DAGA ABDULHAMID ISAH
Shugaban Kwamitin Iyayen yara da Malamai na jihar Kano wato PTA Alhaji Dlhatu Salisu Mai jumuri ya bayyana takaicin yadda wasu daga cikin dalibai a jihar Kano ke tare masu ababen hawa da sunan suna neman a rage musu hanya a lokacin da za su ta fi makaranta.
” Akwai takaici Sosai ka ga dalibi a titi sanye da kayan Makaranta, ya na tare mutanen da bai sansu ba, wai da sunan ya na neman su rage masa hanya ,tabbas akwai hadari a Wannan abun da suke yi”.

“Insha Allahu nan daba jima wa ba Gwanatan jihar Kano zai ta sake kawo motocin daukar Dalibai maza a Mai makon na mata kawai”.
Dalhatu salisu Mai juburi ya bayyana Hakan ne a Lokacin da yake zanta wa da wakilin Kadaura24 a ofishin sa.
Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf -Daga Zainab Nasir Ahmad
Ya ce “Insha Allahu nan ba da jima wa ba shugabncin sa zai kawo karshen wannan lamari.domin Yanzu haka tsare- tsare sun yi nisa sosai da sosai wajen hada kai da gwamnatin jihar Kano karkashin Alhaji Abba kabir Yusuf domin a sama musu motocin da za su rika dibarsu kamar yadda a ka ware iya na mata .
Shugaban kwamitin Iyayen yara da Malamai na jihar kano ya ce sun samar da wani kwamiti da zai rika kewayawa domin gano irin wadancan yaran ta hanyar gano sunansu da makarantarsu har da ajin da suke domin a rika hukuntasu”.
NUJ@70: Gwamnan Kano ya karbi lambar girmamawa daga yan jarida
Mai jumuri ya kara da cewa “Ina kira ga al’ummar jihar Kano da su tallafa mana domin Maganin Wannan matsalar, domin idan muka bar ta haka wallahi za ta iya dawo mana matsalar da zata zo ta same mu Sosai da Sosai”.
Ya Kuma yi kira da daukacin iyayen Yara da su yi kokarin sauke nauyin da ya ke kan su wajen kulawa da ‘ya’yansu domin su kubuta a wajen Ubangiji .