Kungiyar ma’aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar Kano ta mika sakonta na taya murna ga Abbas Ibrahim saboda Sabon mukamin Dan kwamitin Amintattu na kungiya Yan Jarida ta Kasa NUJ .
” Babu shakka kungiyar NUJ ta kasa ta ajiye kwarya a gurbinta , saboda Muna da yakinin Abbas Ibrahim zai iya wannan aikin da aka dora masa kuma Muna da tabbacin ba zai Baiwa mutanen Kano kunya ba”.

Shugaban kungiya RATTAWU na jihar Kano Com. Babangida Mamuda Biyansu ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.
NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami
Com. Babangida Biyamusu ya yabawa shugaban kungiyar NUJ na kasa bisa Wannan kyakykyawan tunanin da ya na baiwa Abbas Ibrahim Wannan mukamin.

” A madadin dukkanin ya’yan kungiyar RATTAWU ta jihar Kano Muna taya dan uwanmu murnar Wannan Sabon matsayin da ya Samu, Muna kuma fatan Allah ya bashir ikon sauke nauyin da aka dora masa”. Inji Shugaban kungiyar RATTAWU ta jihar Kano .