Daga Sani idris Mai waya
Mai Martaba Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi ll y ace Masarautar Kano ta janye Dukkanin Hawan Sallah Babba.
Sarkin yace Matakin Hakan ya biyo Bayan Shawara da Masarautar ta yi da Gwamnatin jihar Kano.

” Mun sami labarin wasu yan Siyasa sun tanadi yara domin ta da zaune tsaye musamman a kan hanyar Sarki ta komawa gida musamman a unguwannin Zage kofar wanbai, to muna sanar da su cewa mun sami labari, kuma mun fada ne don su San mun sani” . Inji Sarki sanusi
Sallah: Baffa Babba ya raba buhu 2,000 na Shinkafa ga Kungiyoyin Tinubu a Kano
Muhammadu Sanusi ll ya bayyana hakan ne yayi ganawa da manema labarai a Fadar Masarautar.
Hakan Kuma Sarkin ya hori Al’umma dasu kaura cewa wasu Jawabai Dake cewar Duk Wanda yayi Sallar Idi wai ba zaiyi ta Juma’a ba.
Yana Mai cewar Al’umma Musulmi dasu ribata da samu Ladan Sallah Idi da Kuma ta Juma’a.
A karshe yayi Fatan Al’umma zasu bukukuwan Sallah Lafiya Kamar yadda ya Kamata.