Babban daraktan cibiyar kula da ingantuwar aiyuka ta kasa (NPC), Hon. Dokta Baffa Babba Danagundi, ya raba buhunan shinkafa 2,000 ga mambobin kungiyar Tinubu Support Group (TSG) a jihar Kano, da nufin tallafawa ya’yan kungiyar a Wannan lokaci da ake tunkarar babbar Sallah
Taron wanda ya gudana a sabon ofishin kungiyar goyon bayan Tinubu da aka kaddamar a Kano, ya samu halartar dimbin jiga-jigan jam’iyyar APC, da magoya bayan jam’iyyar, da jiga-jigan jam’iyyar daga ciki da wajen jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Cibiyar Kula da ingancin aiyuka ta kasa Aminu Abba Kwaru ya aikowa Kadaura24.

A jawabinsa, Dr. Danagundi ya godewa mambobin kungiyar bisa irin biyayya da jajircewa da su ke nunawa. Ya kuma ba su tabbacin cewa wannan somin tabi ne kawai, domin nan gaba kadan za a kaddamar da kashi na biyu na tallafin inda za a rabawa kaya kamar haka:
Motoci 200
Adaidaita Sahu 100
Babura 1,000
Babbar Sallah : Kansilan Lajawa ya raba Naira dubu 500 ga al’ummar mazabarsa
Solar Deep Freezers 1,000
fulawa buhu 1,000
Waken Soya buhu 1,000
Injin Taliya 1,000
Buhun Shinkafa 12,000
Keken dinki 500
Tallafin Kudi na Naira Miliyan 500
Duka wadannan kayayyaki za a raba su ne ga mambobin kungiyoyin Tinubu Support Group a karkashin shirin tallafawa masu kananan sana’o’i na kasa.
Dokta Danagundi ya kuma yi tsokaci kan kashi na farko na shirin bayar da tallafi, wanda ya yi nasarar ba da motoci, babura, keken dinki, injinan noma, dubunnan buhunan shinkafa da fulawa, da dai sauran muhimman kayayyaki ga wadanda suka amfana.
Ya yi alkawarin za a ba da tallafin kashi na uku, na hudu, da na biyar a shekara mai zuwa domin tuni sun fara aiki a kansu.
Babban Darakta ya sake jaddada kudirinsa na samar da aiki da tallafawa yan kungiyar daidai da sabon tsarin sabunta fata na Shugaba Tinubu na ci gaban tattalin arziki da ci gaban kasa.