Daga Isa Ahmad Getso
Shugaban karamar hukumar Rano Malam Naziru Yau, ya yi kira ga al’ummar yankin da su tabbatar sun gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali da lumana,
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito makonni biyu da suka gabata an sami tashin hankali a garin Rano wanda ya yi sanadiyyar mutuwar DPO na garin.

Shugaban karamar hukumar wanda yayi magana ta bakin kakakin karamar hukumar Rano Rt. Hon. Ahmed Abdullahi Jibrin, ya bukaci al’ummar Rano da su manta da abun da ya faru, su rungumi zaman lafiya, hadin kai,da tsoron Allah musamman a Wannan lokaci na Sallah.
“Ina kira ga matasanmu, malaman addini, sarakunan gargajiya, da masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa ba a sami tashin hankali ba a bikin sallar dake tafe ba.”
Shugaban ya kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa an samar da isassun matakan tsaro don kare rayuka da dukiyoyin al’umma alokacin bukukuwan. Ya kuma yi kira ga daukacin al’umma da su ba jami’an tsaro cikakken hadin kai.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na shiyyar Rano Rabi’u Khalil Kura ya aikowa Kadaura24, ya ce Shugaban ua yabawa gwamna Abba Kabeer Yusuf bisa yadda yake samar da ababen more rayuwa da Jagoranci na gari da yake yi a jihar Kano.
Ya kuma bai wa al’ummar yankin tabbacin gwamnatin sa za ta cigaba da samar da karin kayan more rayuwa, ya kuma bukace su da su ci gaba da yi wa kasa addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali.