Daga Ibrahim Sani Gama
Gwamnatin Jihar Kano tace Yanzu Haka Lauyoyin ta sun Fara nazari akan hukuncin Wata kotu a Abuja data rushe zabukan Shugabanin jam’iyyar APC da aka Gudanar a Kano.
Kwamishinan shari’a na Jihar kano Barr. M A Lawan ne ya bayyana hakan ne yayin Wata ganawa da Manema labarai a Kano.
Kadaura24 ta rawaito Cewa Kwamishinan yace sun yi mamakin hukuncin Kuma baza su karbe shi ba , Saboda Lokacin da aka Gudanar da zabukan Shugabanin jam’iyyar na matakan mazabu Babu Wasu da sukai nasu daban don Haka yace basu ga Dalilin da yasa aka rushe shugabanci su Abdullahi Abbas ba.
Barr.M A Lawan yace zasu duba yadda aka yi Masu karar Suka Sami Sakamakon zabukan da aka Gudanar har suka gabatarwa kotu ta abinche dasu.
Masha Allah ai dama ita gaskiya daya ce Allah ya fara tunawa ganduje asiri babu abunda ka gani ma Indai rayuwa ce haka take Sai ma baka da wata dama idan kayi me kyau kaga da kyau