Gwamna Tambuwal yasa Hannu a Dokar Kare hakki Kananan Yara a Sokoto

Date:

Daga Junaidu Sani
  Gwamna Aminu Waziru Tambuwal na jihar Sokoto ya sanya hannu kan dokar kare hakkin yara da nufin inganta rayuwar yara a jihar.
  Da yake jawabi bayan zartar da dokar, Gwamnan ya bayyana dokar a matsayin daya daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin sa ta samu.
 Kadaura24 ta rawaito cewa Gwamnan ya kuma sanya hannu kan dokar hana cin zarafin Bil Adama wadda ta tanadi kawo karshen duk wani nau’i na cin zarafin mata a jihar.
 An rattaba hannu kan dokar ne a wani gagarumin biki da ya samu halartar jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Edward Kallon, da babban jami’in UNICEF a Sokoto, Mista Maulid Warfar, wakilin Plan International da dai sauransu.
 Da yake jawabi, Mista Edward Kallon ya yaba da jajircewar Gwamna Tambuwal da sauran hukumomi da dai-daikun Mutane wajen tabbatar da kafa dokar tare da yin kira ga sauran Jihohin kasar nan da su yi koyi ga Gwamnatin Jihar Sakkwato wajen zartar da dokokin da suka tabbatar da ‘yancin mata da yara.
 Kallon ya ka da cewa EU-UN Spotlight Initiative Project an tsara shi ne don haɓaka haƙƙin daidaikun mutane da tabbatar da yanayin ingantacciyar rayuwar mutane daga kowane nau’i na cin zarafi da ƙarfafa gwaiwar mata da ‘ya’ya mata da ƙwarewar rayuwa a cikin al’umma.
  Gwamnan ya yabawa majalisar dokokin jihar da kwamishinan shari’a Suleiman Usman SAN da kwamishiniyar harkokin mata da yara Hajiya Kulu Sifawa bisa kokarinsu na ganin kudurin ya yi daidai da jahohi ya tanadi ka’idoji da dabi’u na al’adu da addini.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...

Al’ummar Kano ku baiwa AA Zaura hadin Kai domin ya kawo karshen fadan Daba – Baba Yawale

Daga Halima Umar Dogo   Babban Hadimin AA Zaura Alhaji Baba...