Amfani da karfin Soji ba Zai Kawo Zaman lafiya a Africa ba – Abdulsalam Abubakar

Date:

Tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar (rtd), ya ce dole ne kasashen Afirka su sauya salon da suke amfani da shi wajen wanzar da zaman lafiya yana mai cewa amfani da karfin soji ba zai kawo lumana ba.

Ya bayyana haka ne a Abuja ranar Asabar a wani taro da aka gudanar domin karrama shi.

Abubakar ya ce har yanzu nahiyar Afirka na fama da rikice-rikice “iri daban-daban,” wadanda ya ce suna ciki manyan kalubalen da ke addabar nahiyar.

BBC Hausa ta rawaito Jaridar ThisDay, wadda ta ambato shi yana wadannan kalamai ta ce tsohon shugaban kasar ya bukaci shugabannin Afirka su rungumi “sasantawa da yin sulhu” wajen magance rikici-rikice.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NAHCON ta sanar da ranar da za a fara jigilar Maniyatan Nigeria zuwa kasar Saudiyya

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Hukumar kula da aikin hajji ta...

Hisbah ta rushe wajen da aka ce sawun Ma’aiki ya fito a jihar Kano

    Hukumar Hisbah ta kai samame tare da rushe wani...

ƴan siyasa ne su ka kashe Arewacin Nigeria — Inji Gwamna Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa ‘yan...

Shugaban Karamar hukumar Bagwai ya kaddamar da aikn gada ta sama da Naira Miliyan 160

Daga Shu'aibu Sani Bagwai   Karamar hukumar Bagwai a jihar Kano...