Daga Saminu Ibrahim Magashi
Kungiyar Hausawan Nigeria ta ce ba ta goyon bayan gwamnatin tarayya ta yafe ko ta sasanta da yan taa’addan da suke kashe al’ummar arewacin Nigeria .
” Mun sami labarin wasu Shugabannin fulani da sauran masu ruwa da tsaki suna ta bibiyar gwamnatin tarayya da ta yafewa gawurtaccen dan taa’addan da ya yi kaurin suna wajen kashe al’umma wato Bello Turji, inda ya ce kungiyarsu ga ta goyon bayan wannan matakin”.

Shugaban kungiyar Abdullahi Abdullahi ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a jihar Kano ranar litinin.
Ya ce ya zama wajibi Hausawan Nigeria su fito domin nuna damuwarsu kan mawuyacin halin da Hausawa suke ciki, inda ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen domin yakar matsalar tsaro da cin kashin da ake yiwa Hausawa a Nigeria.
” Muna so mu ji inda aka kwana a kisan Killar da aka yiwa Sarkin Gobir da mutanen da aka kone a hanyarsu ta Sokoto da kuma na kwana-kwanan nan Mafarautan da aka kashe a Jihar Edo, har yanzu ba mu komai ba, kuma muna bukatar a dauki matakan da suka dace”. Inji Abdullahi Abdullahi
Shugaban kungiyar Hausawa ta Nigeria ya ce akwai bukatar dukkanin masu ruwa da tsaki a cikin al’umma musamman na yankin Jihohin Katsina Sokoto Zamfara da Kebbi da su tashi tsaye wajen kare kawunansu.
Ya kuma kalubalanci gwamnatin jihar Katsina bisa yadda ta kasa fitowa ta sanar da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu matsalolin tsaro da suka addabi al’ummar jihar, ya ce mai makon a fito da matsalolin sai aka cewa shugaban kasar babu wata matsala.
Daga karshe ya kuma jaddada cewa sun samar da kungiyarsu ne ba don cin mutuncin wasu mutane ko cewa wata kabila yan taa’adda ne ba, sai don hada kan Hausawa da kuma yin magana da murya daya musamman wajen fito da matsalolin da suke damun Hausawa.