Dalilin ya sa Bakwana ya fi kowa dacewar ya zama shugaban APC na Kano

Date:

Daga Zakariya Adam Jigirya

 

Yawan jama’a da kuma shiga lamuran jama’a su ne ginshikin kowacce irin tafiyar siyasa kuma siyasa irin ta jaha ta Kano ta na bukatar mutum mai Ilimin addini dana zamani da Kuma iya mu’amala da kuma iya shawo kan duk wata matsalar daka iya kowa cikas wajen gudanar da tafiyar siyasa.

Kowa ya sani Hon. Mustapha Hamza Buhari Bakwana, ya amsa sunan na shi na bakwana wajen tsayawa akan gaskiya da rikon amana da kuma rungumar ya’ya jamiyyar APC ba tare da nuna kyama ga kowa ba.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Duk wanda ya san tarihin siyasar Mustapha Hamza Buhari Bakwana daga lokacin da ya yi kansila a mazabar shi da kuma irin yadda ya yi ruwa ya yi tsaki wajen yakar wasu jiga-jigai a jam’iyyar PDP a wancan Lokacin .

Gwamnatin mu ba wajen zaman Barayi ba ce – Gwamnan Kano Abba

Tun a wancan lokacin Bakwana ya ci zaben sa ne saboda yawan al’ummar da suka fito su ka kada masa kuri’unsu, wanda hakan ya tabbatar da cewa mutum ne da yake da kyakykyawar mu’amala da mutanensa.

Idan aka la’akari da Wannan nagarta ta shi ba za a yi mamaki ba, idan aka ji dubban al’umma yan jam’iyyar APC a Kano sun fito suna kira a gare shi da ya tsaya takarar shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano.

Muddin Hon. Bakwana ya zama shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano mu na ganin zai hade kan ya’yan jam’iyyar APC a Kano, ta hanyar magance matsalolin cikin gida a jihar wanda hakan zai iya kai jam’iyyar da samun nasara a kakar zabe mai zuwa.

InShot 20250309 102403344

Hon. Mustapha Hamza Buhari Bakwana ya na da gogewa idan akai la’akari da irin mukaman da ya rike a baya.

Idan kuka biyo mu nan gaba za mu kawo muku dalilinmu na cewa Hon. Mustapha Hamza Buhari Bakwana ya fi kowa dacewa ya zaman shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related