Daga Isa Abdullahi Aliyu
Hakimin Kawaji, 𝗔𝗹𝗵𝗮𝗷𝗶 Ibrahim Ado Bayero wanda kuma shi ne Dan Ruwata 𝗞𝗮𝗻𝗼, ya bayyana Jin dadinsa bisa yadda ya ga garin Gwagwarwa na samun cigaba sosai da sosai.
” Babu shakka mun ga abubuwan cigaba a Wannan gari, kuma mun tabbatar wannan cigaban bai samu ba sai da ku ka hada kai, don haka ina fatan za ku cigaba da irin wannan hadin kan don matasa masu tasowa su yi koyi da ku”.

Hakimin ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci al’ummar garin Gwagwarwa dake karkashin dagacin garin Gwagwarwa Alh Usman Sunusi Aliyu.
Za mu kashe sama da biliyan 4 wajen yin aiyukan raya kasa a mazabun Kano – Gwamna Abba gida-gida
A yayin ziyarar, Hakimin ya jaddada kudirinsa na tallafawa al’ummar Gwagwarwa da daukacin gundumar Kawaji baki daya don samar da cigaba mai dorewa..
Alhaji Ibrahim Ado Bayero ya yi fatan al’ummar garin Gwagwarwa za su cigaba da baiwa dagacinsu Alhaji Usman Sanusi hadin kai da goyon baya don samar da karin cigaba a yankin.
Ziyarar Hakimin ta nuna yadda ya damu da sanin halin da al’ummarsa suke cigaba da kuma sadaukar da rayuwarsa don kyautata rayuwar al’ummarsa .
Al’ummar garin Gwagwarwa da karamar hukumar Nassarawa sun yaba da kokarin Hakimin wajen samar da hadin kai da ci gaban kasa