Daga Rukayya Abdullahi Maida
Kungiyar ATM Gwarzo Organisation, wata kungiya ce ta siyasa mai rajin tabbatar da shugabanci na gari, ta kara ce ta aminta da salon shugabancin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu saboda kokarinsa na ciyar da kasa gaba.
Kungiyar ta bayyana hakan ne lokacin da ta gudanar da wani muhimmin taro domin duba ayyukanta tare da jaddada matsayar ta kan muhimman abubuwan ci gaban kasa da kananan hukumomi.

A wata sanarwa da hadimin T Gwarzo kan harkokin kafafen sada zumunta Mansur Umar Man’ash ya aikowa Kadaura24, ya ce Bayan zaman kungiyar ta fitar da abubuwan da tacimma matsaya a kansu kamar haka:
1. Goyon bayan Shugaba Bola Ahmad Tinubu: Kungiyar na kara jaddada goyon bayanta ga salon jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Inda ta ce “Mun amince da sauye-sauye masu mahimmanci da gwamnati ke aiwatarwa don sake fasalin Najeriya don ci gaba mai dorewa. Muna kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da hakuri, hadin kai, da goyon bayan wadannan yunƙurin, domin suna da muhimmanci ga ci gaban ƙasa.
Za mu kashe sama da biliyan 4 wajen yin aiyukan raya kasa a mazabun Kano – Gwamna Abba gida-gida
2. Yabon Hon. Abdullahi Muazu Gwarzo (Babangandu):
Kungiyar ta ATM ta kuma ce tana yabawa Hon. Abdullahi Muazu Gwarzo, dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gwarzo/Kabo, sakamakon irin wakilcin da yake yiwa al’ummar Gwarzo daKabo.
“Yunkurinsa na samar da jin dadi da ci gaban ga yankinsa abun a yaba ne, saboda managartan aiyukan cigaba da yake yi wadanda suke taba rayuwar al’umma sosai da kuma yadda yake aikinsa na dan majalisa.
Kungiyar ta yi alkawarin cigaba da ba shi cikakken goyon baya tare da karfafa masa gwiwa don ci gaba da kan wannan tafarki masu kyau.
3. Fatan Alkhairi ga Nasiru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo:
Kungiyar ATM Gwarzo ta ce tana mika sakonta na fatan alkhairi ga tsohon dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo.
“Kungiyar ATM Gwarzo za ta ci gaba da jajircewa wajen ci gaban babbar jam’iyyar mu ta APC, jihar Kano, da Najeriya baki daya”.