Za mu kashe sama da biliyan 4 wajen yin aiyukan raya kasa a mazabun Kano – Gwamna Abba gida-gida

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Gwamnatin Kano ta ware Naira miliyan dubu hudu da miliyan dari takwas domin baiwa kansiloli damar gudanar da ayyukan raya kasa a mazabunsu.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin taro na musamman da kansilolin jihar Kano 484 a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya bukaci zababbun kansilolin su lalubo ayyukan da al’ummarsu na kasa su ka fi bukata musamman a bangaren ilimi da samar da ruwan sha da gina bandakuna, ya ce gwamnati ta yi wannan tsari ne domin tabbatar da ayyukan raya kasa sun shiga lungu da sako na jihar Kano.

Ya ce gwamnati ta ware kudin a karkashin ma’aikatar kananan hukumomi wanda da zarar kowanne kansila ya bujuro da aikin gwamnati za ta sahhale masa domin fara aiwatarwa.

Gwamnatin mu ba wajen zaman Barayi ba ce – Gwamnan Kano Abba

Ya ce da zarar kansilolin sun aiwatar da ayyukan da ake bukata, gwamnatinsa a shirye take ta sake basu wasu makudan kudaden domin aiwatar da wasu ayyukan na cigaban aluma.

Ya bukaci zababbun kansilolin, da su zamo masu biyayya ga shugabanninsu tare da yin aiki tare bisa gaskiya da rikon amana.

Ya ce gwamnati zata ci gaba da basu dama wajen lalubo matan da zu amfana da tallafin da gwamnatinsa take bayarwa a kowane karshen wata kasancewar sune suka fi kusaci da al’uma.

Kazalika gwamna Abba Kabir Yusuf ya Kara da cewa su ma nadaddun kansiloli, gwamnatinsa ba za ta barsu a baya ba, zata samar da hanyoyin da za’a tallafa musu.

InShot 20250309 102403344

Daga nan ya gargadi masu taba muhibbar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da cewa suna yin hakan ne domin bata masa suna, tare da cewa suna da yankinin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso duk ya fisu nagarta.

A baya bayan nan ne dai majalisar zartaswar jihar Kano ta ware sama da naira biliyan 15 domin biyan tsoffin kansilolin da suka yi aiki a gwamnatin tsohon gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga shekarar 2014-2024 hakkokinsu da gwamnatin baya ta gaza biyansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...