Daga Rukayya Abdullahi Maida
Wasilah Ibrahim Ladan, sakatariyar kungiyar mata โyan jarida ta kasa (NAWOJ) kuma babbar mai bayar da rahoto a gidan rediyon Najeriya, ta samu lambar yabo ta Kasa da kasa bisa jajircewarta wajen gudanar da aikinta.
Wannan babbar lambar yabo ana karrama yan jaridun da suka nuna kwazo da jajircewa da kuma sadaukar da kai wajen gabatar da aikinsu na aikewa da rahoto.

Gagarumin gudunmawar da Wasila Ladan ta bayar wajen inganta zamantakewar alโumma ta kafafen yada labarai da bayar da shawarwari kan ilimin โyaโya mata, su ne su ka sanya har ta sami wannan lambar yabo a kasar Amuruka.
An yi la’akari da dabarun da ta ke amfani da su wajen Isar da sakonnin da suka shafi wayar da kan ya’ya mata.
Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano
Kyaftin Francis Asapokhai, shugaban kungiyar Prezens for Charity, da Misis Catherine Utsalo, mataimakiyar shugaban, sun bayyana jin dadinsu kan yadda Wasila Ladan ya samu gagarumar nasara a aikin jarida.
“Babu shakka ta sami wannan lambar yabon ne bisa chanchanta saboda yar jarida ce da ta nuna kwarewa wajen gudanar da aikinta”.
Ita ma a na ta jawabin bayan karbar lambar yabon Wasila Ladan, ta bayyana jin dadin ta, inda ta ce, “Na yi matukar Jin dadi da ba sami wannan babbar karramawar. Sannan ina godewa Kasar Amuruka da kungiyar da suka ba n wannan lambar yabo, haka zalika ina godewa ga Salma Yusuf shugaban sashin wasanni ta Freedom Radio
Kano, kuma Jami’in yada labarai ta
U20 Falconet.