Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
2, Zulqida 1446
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar hutu domin baiwa ma’aikata damar gudanar da bikin ranar ma’aikata ta bana, wadda ake gudanarwa duk ranar 1 ga watan Mayu na kowacce shekara.

Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida ne ya sanar da hutun a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Gwamnatin Kano ta shiryawa Limaman masallatan juma’a Bita
Tunji-Ojo ya yabawa ma’aikatan Najeriya bisa jajircewa da sadaukarwar da su ke yi, wajen ganin kasar ta samu cigaban da ake fata .
Ya bukaci ma’aikatan Nigeria da su za mo masu dabi’ar kirkira da yin aiki mai inganci don cigaban tattalin arzikin Nigeria.