Yansanda sun kama ‘yan fashin daji 17 Makamai a Nigeria

Date:

Daga Ummahani Abdullahi Adakawa

 

Rundunar ‘yansandan Najeriya ta ce ta kama mutum 15 da take zargi da aikata fashi da kuma garkuwa da mutane a faɗin ƙasar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Olumiyiwa Adejobi ya ce dakarunsu sun yi nasarar ƙwace makamai da dama.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Sanarwar ta ce rundunarta ta Special Tactical Squad (STS) ce da taimakaon mafararuta da ‘yan sa-kai ta yi nasarar kama ‘yanfashi huɗu a jihar Taraba ranar 25 ga watan Afrilu, sannan ta ƙwace bindigogi uku.

A jihar Kaduna kuma, wani samame da dakaru suka kai ya yi sanadiyyar kama mutum biyar da zargin aikata fashi. An kama ɗauke da bindigogi ƙirar AK-49 da AK-47 huɗu.

Gwamnatin Kano ta shiryawa Limaman masallatan juma’a Bita

“A ranar 17 ga watan Afrilun kuma, dakarun sun kama wani mai suna Isa Ibrahim, wanda ya amsa cewa ya koma Kaduna ne domin kafa wata sabuwar dabar ‘yanfashi bayan kama abokan aikinsa a jihar Kwara,” in ji sanarwar.

InShot 20250309 102403344
“Ranar dai, samamen da jami’ai suka kai a ƙauyen Lamido ya yi nasarar kama ‘yanfashi biyu, waɗanda suka amsa laifukan fashi.

“A ranar 18 ga watan, ‘yansandan jihar [Kaduna] sun kama wasu masu safarar bindigogi ɗauke da binidigogin AK-47 biyu, daga baya kuma suka kama wani ɗauke da bindigogi biyu ƙirar gida da wata doguwar sarƙa a cikin buhu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...