A Gaggauce: Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokokin kirkirar sabbin ma’aikatu 4

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokokin kirkirar sabbin ma’aikatu gwamnatin jihar har guda hudu.

Gwannan ya ce kirkirar sabbin ma’aikatun zai kara taimakawa wajen inganta cigaban jihar Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24 ranar Juma’a.

InShot 20250309 102403344

Sanarwa ta ce sabbin ma’aikatun da aka sanyawa dokokinsu hannu su ne kamar haka:

1. Kano State Protection Agency (KASPA)

2. Kano State Signage and
Advertisement Agency (KASIAA)

Mawaki Rarara zai angonce da Jaruma Aisha Humairah

3. Kano State Information and Communication Technologies Development Agency (KASITDA)

4. Kano State Small and Medium Enterprises Development Agency (KASMEDA)

Wadannan dokoki sun shiga cikin kunshin dokokin da jihar Kano ta ke da su, wadanda ake da yakinin za su taimaka matuka wajen inganta masana’antu da kula da tallace-tallace da kuma kare mutane da dai sauransu.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Gwamna Yusuf ya ce sanya hannu kan dokokin wata gagarumar nasara ce ga gwamnatinsa a kokarinta na samar da cigaba mai dorewa a jihar Kano.

Ya ce sabbin ma’aikatun za su taka muhimmiyar rawa wajen samar da aikin yi ga matasa da jawo hankalin masu zuba hannun jari da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Adam A Zango ya sake Aurar Jarumar Kannywood

Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa, Kannywood, Adam A....

NNPP ta yi watsi da sakamakon Zaben Ghari da Tsanyawa a Kano

Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta ƙi amincewa da...

Kwankwaso ya yi tsokaci game da zaben cike gurbi da akai a Kano

Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana...

A Hukuma ce INEC ta bayyana sakamakon zabukan cike gurbi da aka yi a kano

Hukumar zabe mai zamanta ta Kasa ta bayyana Dan...