Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Tsohon shugaban Nigeria Muhammad Buhari ya ce kadarorin da ya mallaka kafin ya zama shugaban kasa har gama shugaban kasa ba su karu ba.
A wata sanarwa da kakakin tsohon shugaban kasar Mallam Garba Shehu ya fitar ya ce Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da gwamnonin APC da suka kai masa ziyara a gidansa da ke Kaduna.
Tsohon shugaban ya shawarci gwamnonin na APC su rungumi aniyar hidimta wa al’umma, yana mai cewa shugabanci cike yake da tarin ƙalubale da kuma dama, kuma haɗa abubuwan biyu ne zai ciyar da ƙasa gaba.

Muhammadu Buhari ya ce kadarar da ya mallaka tun kafin ya hau mulki ba ta ƙaru ba har bayan saukarsa daga mulki a watan Mayun 2023.
Musa Iliyasu Kwankwaso, Rabi’u Sulaiman Bichi sun kama aikin da Tinubu ya ba su
Buhari ya godewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu bisa yadda ta gyara masa gidansa da ke Kaduna, inda ya bayyana cewa duk da ginin ta wajen ba a kaya ta shi ba, amma a cikin gidan an inganta ginin gidan sosai.
Ya godewa gwamnonin bisa ziyarar da suka kai masa, inda ya ce ya yi aiki da da dama daga cikinsu, wasu kuma sababbi ne a wajensa.