Daga Sani Idris maiwaya
Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Surajo Ibrahim Imam ya kaddamar da aikin hanya da za’a kashe sama da Naira miliyan 197 a yankin Gobirawa Daiba dake karamar hukumar.
Da yake Kaddamar da Aikin Shugaban Karamar Hukumar ya bukaci dan kwangilar da zai yi aikin da ya yi aiki mai inganci da nagarta Sannan ya sanya matasan yankin a cikin wadanda za su yi Aikin a wasu bangarorin Aikin.

“Mun ware wadannan kudaden ne domin gudanar da aikin Wannan hanya mai matukar muhimmancin gaske ga al’ummar, kuma Muna da yakinin idan an kammala aikin al’ummar wannnan yankin da makwaftansu za su ji dadin aikin, domin zai taimaka wajen rage musu wahalhalun da suke fuskanta a yanzu da kuma bunkasa tattalin arzikinsu”. Inji Suraj Imam
Alhaji Surajo Imam ya kuma ce kamfanin Nomora Integrated service ne aka Baiwa kwangilar aikin kuma an Riga an biyasu kaso hamsin cikin dari na kudin Aikin.
Rundunar Yansanda ta ba da sabon umarni kan gayyatar da ta yi wa Sarki Sanusi
Ya yi kira ga al’ummar yankin da su baiwa dan kwangilar hadin kan da ya dace domin samun nasarar kammala aikin akan lokaci.
Suma wasu mazauna Yankin Alhaji Mustapha Abdulmajid A.Z da Naziru Gambo sun bayyana farin cikin Su bisa Samun wannan Aikin suna Masu cewar Aikin hanyar ya Dade Yana ci musu tuwo a kwarya
A karshe Cikin wata Sanarwa da Jami’ar Hulda da Jama’a ta Karamar Hukumar Dala Hassana Aminu ta sanyawa hannu tace wakilin kamfanin da zaiyi Aikin Alhaji Tasiu yayi Alkawari zasuyi Aikin Mai inganci da nagarta Kuma zasuyi Shi akan Lokaci.