Mun gamsu da yadda malamai da daliban su ka koma makarantu – Gwamnatin Kano

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Gwamnatin jihar Kano ta yaba da yadda Ι—aliban makarantun firamare da sakandire suka koma makarantunsu a yau litinin 7 ga watan Afrilu domin fara karatun Zango na uku na shekarar 2025.

Kwamitin da ke sa ido kan makarantun sun bayar da rahoton cewa malamai da daliban makarantun da su ka ziyarta sun koma makarantunsu yadda ya kamata.

InShot 20250309 102403344
Talla

A Wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa Malamai da daliban sun fara zuwa makarantun da misalin karfe 7:30 na safe.

Shugaban K/H Dala ya kaddamar da aikin hanya na kusan Naira miliyan 200 a mazabar Gobirawa

β€œMun ga yadda malamai suka fara Shirye-Shiryen ba da karatu, tare da tsaftace harabar makarantunsu domin fara karatunsu cikin sauki.” Inji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa kwamishinan ilimi na jihar Dr. Ali Haruna Makoda ya yaba wa mahalarta malamai da daliban, ya kuma bukaci shugabanni da malamai da su kara himma wajen gudanar da aikinsu yadda ya dace.

Ya godewa iyaye bisa hadin kan da suka ba su, ya kuma yi alkawarin gwamnati za ta cigaba da inganta harkar ilimi a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related