Yawan Ciyo bashin ne ya Jefa Nigeria Cikin Mawuyacin hali – Nastura Ashir

Date:

Daga Rabi’u Sani Hassan

Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Cigaban Arewacin Nigeria Nastura Shariff Ashir ya bayyana Cewa yawan ciyo bashin da Shugaban Kasa Muhammad Buhari ke yi shi ne musabbabin kuncin Rayuwar da talakawan Kasar nan suke fuskanta.
Nastura Ashir ya bayyana hakan ne yayi Wata tattaunawa ta Musamman da yayi da wakilin Kadaura24 dan gane da Matsalolin da a Yanzu suke damun yan Kasar nan.
Nastura Ashir yace Saboda Sanin illar da Ciyo bashin kasashen turawa ke da shi yasa masana tattalin arziki Suka baiwa shugaba Buhari Shawarar kada ya ciwo bashin, Amma ya ki Kuma Yanzu ga Abun da Suka fada Yana tabbata.
Tun a Watan satumbar Wannan shekarar, duk Naira daya in ka dauke ta Kobo chasa’in da bakwai Cikin ta ana Amfani da shi ne wajen biyan kudin Ruwan bashin da Nigeria ta ciyo a gurare daban-daban a Duniya”. Inji Nastura Ashir
Yace daga satumbar Shekarar Nan Zuwa Yanzu Buhari ya Nemi sahallewar Ciyo Wasu basussukan, Inda yace daga nan Zuwa Watan janairun sabuwar Shekara ta 2022 Bincike ya nuna kudaden harajin da Kasar nan take karba dari bisa dari ba zasu iya biyan kudin Ruwan bashin da ake bin Kasar nan ba.
Nastura ya Kara da Cewa shi bashin da ake bin Nigeria a ka’idarsa sai an Shekara 10 ana biyan kudin Ruwan bashin,Sannan Kuma a Shekara 30 na biyan kudin bashin.
“Bankuna da Sauran kasashe baza su yarda su cigaba da baiwa Nigeria bashi ba,har sai an dorawa yan kasar Wata musifa an Mai da su kamar bayi yadda zasu ga cewar harajin da Kasar take tarawa Zai iya biyan kudin Ruwan bashin da zasu bayar” a cewar sa
Shugaban Kungiyar Gamayyar Kungiyoyin Cigaban Arewacin Nigerian yece hakan tasa tun tuni masana suka baiwa Gwamnatin Shawarar kada a Ciyo bashin Saboda Gudun kada Kasar nan ta Koma bayan turawa, Amma Shugaba Buharin yaki amince da hakan Wanda Kuma hakan ne ummu aba’isin mawuyacin halin da al’umma Suka tsinci kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...