Bayan Tarwatsa Wani Gari a Zamfara Yan Bindiga Sun Sace Mutane masu yawa

Date:

Rahotanni daga Zamfara, na cewa Gomman mutane sun tsere daga ƙauyen ‘Yan Ɓuki cikin ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, bayan wani harin ‘yan fashin daji ya yi sanadin hallaka mutum bakwai.

Wani mazaunin ƙauyen da shi ma ya tsere zuwa Gusau ya ce da misalin karfe 12 na rana ne maharan suka shigo garin, tare da bude wuta, sun kuma shiga gidaje suna fito da mata da kananan yara da maza har da tsofaffi sama da 50, suka yi cikin daji da su, sannan sun ƙone musu dukiyar da ba a san adadinta ba.

Mutumin ya ce su ma Allah ne ya kubutar da su, suka samu tserewa tare da shiga motar da ta kai su birnin Gusau, ”bayan mutanen da suka tafi da su, sun kuma kashe mutum bakwai, ciki har da dan uwana uwa daya uba daya mai suna Abdullahi.”

“Har cikin daki suka shiga suka fito da shi, yana turjewa amma haka suka harbe shi a baya da kuma makoshinsa,” in ji mutumin da bai so a bayyana sunansa ba.

BBC Hausa ta rawaito kawo yanzu ‘Yan sanda ba su tabbatar da wannan harin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...